Daga Salamah Dan Akwa'a - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hann...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum yana ci da hannunsa na hagu, sai ya umarce shi da ya ci da hannunsa na dama, s...
Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa,...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya ci tafarnuwa ko albasa zuwa masallaci, dan kada ya cutar da 'yan uwansa daga w...
Daga Sahlu ɗan Mu'azu ɗan Anas daga babansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci abin ci sai ya ce:...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya ci wani abinci da ya godewa Allah, babu wani iko gareni a samun abin...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana...
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata aagre shi ya kasance idan zai yi atishawa: Da farko: Yana ɗora hannunsa, ko tufafinsa akan bakinsa; da...
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana son azo wa rangw...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana son azo wa rangwaminSa wadanda ya shara'antasu, na sauki a ci...

Daga Salamah Dan Akwa'a - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wani mutum ya ci a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da hannun hagunsa, sai Ma’aikin Allah ce da shi: "Ka ci da hannun damanka ." Ya ce: Ba zan iya ba. Ya ce: "Ba za ko ka iya ba", ba abin da ya hana shi sai girman kai, ya ce: Bai kara daga shi zuwa bakinsa ba.

Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa", kuma cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an zo masa da wata tukunya a cikinta akwai korren abubuwa daga maɓungura ƙasa, sai ya ji wari daga gareta, sai ya yi tambaya sai aka ba shi labarin abinda ke cikinta na maɓungura ƙasa, sai ya ce ku kusantar da ita ga wani daga sahabbaina wanda ke tare da shi, lokacin da ya ganta sai ya ƙyamaci cinta, ya ce: "Ka ci domin cewa ni ina ganawa da wanda ba ka ganawa (da shi)".

Daga Sahlu ɗan Mu'azu ɗan Anas daga babansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi.

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda Allah Yake nufinsa da alheri zai shafeshi da rashin lafiya (zai jarrabeshi)".

Daga Abu Sa'id Alkhudri da Abu Hurarira - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba abinda yake samun musulmi na wahala ko rashin lafiya ko bakin ciki ko takaici ko cuta ko bakin ciki har kayar da zai taka, sai Allah ya kankare masa kurakuransa da su".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi".

Daga Suhaib - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.

Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini ya kai yammaci yana kafiri, ko ya yammanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai sayar da addininsa da wata haja ta duniya".

Daga Mu’awiya - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa; Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.