Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana son azo wa rangwaminSa, kamar yadda yake son azo wa yin aiki a asalinsa".
Ibnu Hibban ne ya Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana son azo wa rangwaminSa wadanda ya shara'antasu, na sauki a cikin hukunce-hukunce da ibadu, da saukakawa a cikinsu ga wanda aka dorawa shari'a - kamar kasarun sallah da kuma hada su a halin tafiya -. Kamar yadda cewa Shi Yana son azo wa azimarSa, daga al'amura wajibai; domin umarnin Allah a rangwame da wajibai daya ne.
Hadeeth benefits
Rahamar Allah - Madaukakin sarki - ga bayainSa, kuma cewa Shi - tsarki ya tabbatar maSa - yana son a aikata abinda Ya shara'anta shi na rangwame.
Cikar wannan shari'ar, da kuma dauke kunci ga musulmi.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others