Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce...
Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa addu'a ita ce ibada, to, wajibi ne ta zama dukkaninta abar tsarkakewa g...
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe.
Nana A'isha uwar Muminai Allah Ya yarda da ita, tana ba da bayanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana tsananin kwaɗay...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta...
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani musulmi da zai yi wat...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa; Musulmi idan ya roƙi Allah ya roke shi wata bukata wacce ba zunubi ba ce...
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Akwai darajoji ɗari a cikin aljann...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljannar Lahira akwai darajoji da matsayi ɗari, tsakanin kowace da...
Daga Nu'uman ɗan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".
Daga Abu sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani musulmi da zai yi wata addu'a wacce babu zunubi a cikinta, kuma babu yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi ɗayan abu uku: Kodai Ya gaggauto masa da (amsa) addu’ar sa, ko kuma Ya tanadar masa ita sai ranar alƙiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce: Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah Shi ne Mafi yawaitawa".
Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Akwai darajoji ɗari a cikin aljanna, tsakanin kowace daraja kamar tsakanin sama da ƙasa ne, Firdausi it ce mafi ƙololuwarsu (a daraja), kuma daga nanne ƙoramun aljanna suke ɓuɓɓugowa, kuma a samanta ne Al’arshi yake. Idan zaku roƙi Allah to ku roƙe shi Firdausi».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa" sai na ce: Ya Manzon Allah, mun yi imani da kai da kuma abinda ka zo da shi, shin kana jin tsoro akanmu ne? ya ce: "Eh, lallai zukata suna tsakanin yatsu biyu daga yatsun Allah Yana jujjuyasu yadda Ya ga dama".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa: ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na, kuma Ka gyara mini duniya ta wacce na ke rayuwa a cikinta, Ka kuma gyara mini lahira ta wacce a cikinta ne makoma ta take, Ka sanya rayuwa (ta zamo) ƙarin duk wani alheri gareni, kuma Ka sanya mutuwa ta zamo hutu ce a gare ni daga dukkan wani sharri’’.
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai kasance yana barin waɗannan addu'o'i ba lokacin da ya yi yammaci ko ya wayi gari: "Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira, ya Allah lallai ni ina roƙonKa rangwami da lafiya a Addini na da duniya ta da iyalaina da dukiyata, ya Allah Ka suturta al'aurata - ko: al'aurorina Ka amintar da tsorona, ya Allah Ka kiyayeni ta gabana, da bayana, da damana, da haguna, da samana, ina nemn tsarinKa kada a yaudareni da kisa ta ƙarƙashina".
Daga (Nana) A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya koya mata wannan addu'ar: "Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba. Ya Allah ina roƙonKa mafi alherin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya roƙeKa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin abin da bawanKa kuma AnnabinKa ya nemi tsarin Ka da shi, ya Allah ina roƙonKa aljanna da abin da yake kusantota na magana ko aiki, kuma ina neman tsarinKa daga wuta, da abin da yake kusantota na magana ko aiki, ina rokonKa Ka sanya dukkan hukuncin da Ka hukunta gare ni ya zama alheri".
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku".
Daga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo".
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannuna, sai ya ce: "Ya Mu'az, wallahi lallai ni ina sonka", sai ya ce: "Ina yi maka wasicci ya Mu'az bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa".