- waɗanda su ne mafi muhimancin abu; saboda haka ne Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara addu'a da shi.
- Addini (shi ne) ƙashin bayan mutum da zai hana shi kowane sharri.
- Addu'a da al'amura na duniya saboda gyaruwar Addini da lahira.
- Ba'a ƙin burin mutuwa dan tsoro daga fitina a cikin Addini, ko roƙon Allah mutuwa akan shahada.