Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Lallai masu adalci a wurin...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa waɗanda suke hukunci da adalci da gaskiya a tsakanin mutane waɗanda suk...
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta babu cutarwa, wanda...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa tunkuɗewa kai da wasu cuta yana wajaba gargwadon nau'o'inta da yadda ta bayy...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kaɗai kwatankwacin abokin zama na g...
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya buga misali ga nau'i biyu na mutane: Nau'i na farko: Abokin zama da aboki na gari wanda yake shiryar...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasi...
Ɗaya daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - ya nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da shi a kan wani abin da...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba,...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa ƙarfi na haƙiƙa ba ƙarfin jiki ba ne, ko wanda yake ka da wasu ƙarfafa, kaɗai...

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Lallai masu adalci a wurin Allah suna kan munbarirrika na haske, a daman Ubangiji Al-Rahman - Mai girma da ɗaukaka - su duka hannayensa biyun na dama ne, waɗanda suke adalci a hukuncinsu da iyalansu da abin da suka jiɓinta".

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu cuta babu cutarwa, wanda ya cutar Allah Zai mayar masa da sakamakon cutar a kansa, wanda ya tsananta Allah Zai mayar masa da sakamakon tsanantawar a kansa".

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi, maɗaukin alimiski: Kodai ya baka, ko kuma ka saya daga gare shi, ko kuma ka samu ƙanshi mai daɗi daga gare shi, mai busa zugazugi kuwa: Kodai ya ƙona kayanka, ko kuma ka samu mummunan ƙanshi daga gare shi".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: "Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".

Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce: "Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi".

Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci".

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba".

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".

Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".

Daga Jabir ɗan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kowa ne aikin alheri sadaka ne".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta, kowanne yinin da rana ta fito a cikin sa da (mutum) zai daidaita tsakanin mutune biyu sadaka ne, kuma ya taimaki mutum game da dabbar sa; sai ya ɗora shi a kanta, ko ya ɗauke masa kayan sa a kanta, to, sadaka ne, kuma kalma mai daɗi sadaka ce, kuma kowanne taku da zai yi zuwa sallah sadaka ne, kuma ya kau da ƙazanta daga hanya sadaka ne".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".