- Tsarin ƙasusuwan ɗan Adam da lafiyarsu yana daga mafi girman ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki - akan mutum, to kowanne ƙashi daga cikinsu yana buƙatuwa zuwa ga sadaka daga gare shi a karankansa dan godiyar wancan ni'imar ta cika.
- Kwaɗaitarwa akan jaddada godiya a kowacce rana dan dawwaamar da waɗancan ni'imomin.
- Kwaɗaitarwa a kan dawwama da nafilifili da sadakoki Kowacce rana.
- Falalar yin sulhu tsakanin mutane.
- Zaburarwa akan taimakon mutum ga ɗan'uwansa; domin taimakonsa gare shi sadaka ne.
- Zaburarwa akan halartar sallar jam'i da tafiya zuwa gareta, da raya masallatai da hakan.
- Wajabcin girmama hanyoyin musulmai ta hanyar nisantar da abinda zai kware su ko ya cutar da su.