- Ibnu Daƙiƙul Eid ya ce: Wannan hadisi ne mai girma, mai tattarowa ne ga nau’ukan ilimummuka da ƙa'idoji da ladubba, a cikinsa a kwai falalar biyan buƙatun musulmai da anfanar da su da abinda ya sawwaƙa, na ilimi, ko dukiya, ko taimako, ko nuni da wata maslaha, ko nasiha, ko wanin haka.
- Kwaɗaitarwa a cikin yalwatawa wanda ke cikin matsi.
- Kwaɗaitarwa akan taimakon bawa musulmi, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana taimakon mai taimako gwargwadan taimakonsa ga ɗan uwansa.
- Daga suturta musulmi: Rashin bibiyar al'aurarsa, haƙiƙa an ruwaito daga sashin magabata ya ce: Na riski wasu mutane basu da wasu aibuka, sai suka ambaci aibukan mutane, sai mutane suka ambata musu aibuka, kuma na riski wasu mutane sun kasance suna da aibuka, sai suka kame daga aibukan mutane, sai aka manta da aibukansu.
- Barin munkari da rashin canja shi bai zama daga lazimtar suturta mutane ba, domin in ya canja ya suturta, wannan a cikin haƙƙin wanda ba'asan shi da ɓarna ba da kuma zarcewa a cikin shisshigi ba, wanda aka san shi da hakan to shi ba'a son suturta shi, kai za'a kai al'amarinsa zuwa ga hukuma, idan bai ji tsoron ɓarna ba daga hakan; hakan domin suturta shi zai ruɗar da shi akan ɓarnar, kuma zai sa shi ƙarfin hali akan cutar da bayin Allah, kuma zai sa waninsa ma ƙarfin hali daga ma'abota sharri da tsaurin kai.
- Kwaɗaitarwa akan neman ilimi da karatun alƙur'ani da mudararsa.
- AlNawawi ya ce: A cikin wannan akwai dalilin taruwa akan karatun alƙur'ani a cikin masallatai... an riskar da masallaci a tabbatar da wannan falalar, taruwa a cikin wata makaranta ko zaman dako da makancin su in Allah - Maɗaukakin sarki - Ya so.
- Sakayya kawai Allah Ya jeranta ne akan ayyuka ba'a kan nasabobi ba.