Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sa...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka sai ya ce: Ya ku mutane lallai cewa Allah haƙiƙa ya...
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (sh...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - yana ƙin mai tsananin husuma, kuma mai y...
Daga Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan musulmai biyu s...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, kowanne daga cikinsu yana...
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya ɗaga makami a kammu, to...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana gargaɗarwa daga ɗaukar makami a kan musulmai, don tsorata su ko yi musu ƙwace, wanda ya a...
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haramcin zagin matattu da afkawa a cikin mutuncinsu, kuma wannan yana daga munanan...
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Lallai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi wa mutane huɗuba a ranar buɗe Makka, sai ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah Ya kawar muku da wautar Jahilci da jiji da kai da iyayen da take sa su, sabo da haka mutane sun kasu biyu: Mai biyayya ga Allah kuma mai tsoronSa mai girma a wajen Allah, da kuma fajiri taɓaɓɓe wulaƙantacce a wajen Allah, mutane 'ya'yan (Annabi) Adam ne, kuma Allah Ya halicci Annabi Adam daga turɓaya, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ya ku mutane lallai Mun halicce ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama'a da ƙabilu don ku san juna, lallai mafi girmanku a wurin Allah shi ne mafificinku a tsoron Allah, lallai Allah Masani ne kuma mai ba da labari [Al-Hujrat: 13].
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya ce: "Lallai mafi ƙiyayyar mutane a wurin Allah (shi ne) mai taurin kai mai tsananin husuma".
Daga Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu"
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kada ku zagi matattu; domin cewa sun iso zuwa abin da suka gabatar".
Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba ya halatta ga mutum ya ƙauracewa ɗan uwansa sama da dare uku, suna haɗuwa, sai wannan ya kau da kai, wannan ma ya kau da kai, mafificinsu (shi ne) wanda zai fara yin sallama".
Daga Sahal Dan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk wanda ya lamunce min abinda ke tsakanin mukamukansa biyu da abinda ke tsakanin kafafuwansa biyu zan lamunce masa aljanna".
Daga Abu sa'id AlKhudr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance ya yi yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yaƙi goma sha biyu - ya ce: Na ji abubuwa hudu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka ƙayatar dani, ya ce: "Kada mace ta yi tafiya, tafiyar kwana biyu sai da mijinta tare da ita ko muharraminta, Babu azumi a ranaku biyu: Karamar sallah da babbar sallah, kuma babu sallah bayan asuba har sai rana ta bullo, kuma babu bayan la'asar har sai ta fadi, kuma ba'a daure sirdi (nikar gari domin tafiya) sai a masallatai uku: Masallaci mai alfarma, da masallacin Kudus, da masallacina wannan".
Daga Usama Ɗan Zaid Allah Ya yarda da su, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: "Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi".
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".
Daga Mu'awiyya alKushairi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce;
"Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki".