- Rashin halaccin tafiyar mace ba tare da muharrami ba.
- Mace ba muharrama ba ce ga mace a tafiya; Saboda fadinsa: "Mijinta ko muharraminta".
- Dukkan abinda ake kira tafiya to mace an hanata ta yi ba tare da miji ko muharrami ba, wannan hadisin ya kasance ne gwargwadan halin mai tambaya da wurinsa.
- Muharamin mace shi ne mijinta ko wanda ya haramta ta aure shi har abada, saboda kusanci kamar uba da Da da baffa da kawu.
- Ko shayarwa kamar uba na shayarwa da baffa na shayarwa, ko surukuta kamar baban miji, kuma ya zama musulmi baligi mai hankali amintacce, domin abin nufi daga muaharrami kare mace da tsareta da tsayuwa da sha'aninta.
- Kulawar shari'ar Musulunci da mace, da kareta da tsareta.
- Rashin ingancin sallar nafila kowacce bayan sallar Asuba da la'asar, an toge daga hakan rama farillan da suka wuce, da masu sabubba, kamar gaisuwar masallaci da makamancin hakan.
- Sallah ta haramta bayan bullowar rana kai tsaye, domin babu makawa sai ta dago gwargwadan goron mashi, da abinda ya yi kusa na mintina goma zuwa sha biyar a kusance.
- Lokacin la'asar yana mikewa zuwa faduwar rana.
- A cikinsa akwai halaccin daure sirdi (domin tafiya) zuwa masallatai uku.
- Falalar masallatai uku da fifikonsu akan wasunsu.
- Rashin halaccin tafiya dan ziyartar ƙaburbura koda ya kasance ƙabarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ne, amma ziyararsa ta halatta ga wanda yake a Madina, ko ya zo Madina dan wata buƙatar da aka shara'anta ko aka halatta.