- Kwadaitarwa akan lazimtar tsoron Allah, da barin shagaltuwa da zahirin duniya da kawarta.
- Kiyayewa daga fitinuwa da mata, na kallo ko sakaci da cakuduwarsu da maza manisanta, ko wanin hakan.
- Fitinar mata tana daga mafi girman fitintinu a duniya.
- Wa'azantuwa da daukar izina daga al'ummun da suka gabata, abinda ya faru ga Banu isra'ila zai iya faruwa ga wasunsu.
- Fitinar mata idan ta kasance mata ce to ita zata iya dorawa mutum ciyarwar da ba zai iya ba, sai ta shagaltar da shi daga neman al'amuran Addini, ta kuma dora masa halaka a neman duniya, idan kuma manisanciya ce to fitinarta da rudar da maza ne da karkatar dasu daga gaskiya idan sun fita sun cakuda dasu, musanmama dai idan sun zama matsiraita masu shiga ta nuna tsiraici, wannan zai iya kaiwa zuwa afkawa a cikin zina a girmansa, to yana kamata ga mumini ya yi riko ga Allah, da kuma kwadayi gareShi don kubuta daga fitinarsu.