Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba].
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana aske wani sashi na kai da kuma barin wani sashin. Hanin gamamme ne ga Maza ƙanana da ma...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Rantsuwa mai sa anfan...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi akan rantsuwa da kuma yawaita ta koda ta kasance akan gaskiya ne a siye da siyar...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku rage gashin baki, ku cika gemu".
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umarni da rage gashin baki, kuma kada a barshi, kawai a rageshi, kuma a kai matuƙa a haka...
Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mutum ya kalli al'au...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana namiji ya kalli al'aurar namiji, ko mace ta kalli al'aurara mace. Al'aura: Ita ce...
Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙo...
Mummunar magana ko mummunan aiki ba su kasance cikin dabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, bai nufe shi ba, kuma bai gangant...

Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su: Ma’aikin Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya hana askin banza [barin wani wuri a kai da ba a aske ba].

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce".

Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku rage gashin baki, ku cika gemu".

Daga Abu sa'id Al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada wani mutum ya kalli al'aurar wani mutum, ko mace ta kalli al'aurar wata mace, kuma kada wani namiji ya lulluɓa da wani mutum a cikin mayafi ɗaya, kuma kada wata mace ta lullaɓa da wata mace cikin mayafi ɗaya".

Daga Abdullahi Bn Amr -Allah Ya yarda da su- ya ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, bai taɓa kasance wa mai alfasha ba, ko mai ƙoƙarin alfasha ba, ya kasance yana cewa: Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku.

Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare.

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.

Sa’ad Ɗan Hisham Ɗan Amir ya ce: A Lokacin da ya zo wurin Nana Aisha Allah Ya yarda da ita: Ya uwar Muminai! Ki ba ni bayani kan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: A she ba ka kasance kana karanta Alƙur’ani ba ?? Na ce: Ina karantawa, ta ce: To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne.

Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka.

Daga Shaddadu ɗan Aws - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Abubuwa guda biyu na haddacesu daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu, idan za ku yi kisa, to, ku kyautata kisan, kuma idan za ku yi yanka, to, ku kyautata yankan, kuma ɗayanku ya wasa wuƙarsa, ya hutar da abin yankansa".