- Hani daga kallon al'aurori in banda miji da matarsa.
- Kwaɗayin Musulunci akan tsarkake jama'a da rufe hanyoyi masu kaiwa ga alfasha.
- Halaccin duba al'aura idan buƙata ta kama ga hakan, kamar magani da makamancinsa akan ya kasance bada sha'awa ba.
- Musulmi an umarce shi ne da suturta al'aurarsa da rintse ganinsa daga al'aurar waninsa.
- An keɓanci hani da maza tare da maza da mata tare da mata; Domin ya fi ja ga duba da yaye al'aurori.