- Girmama al'amarin rantsuwa da Allah, kuma cewa ita ba ta kasancewa sai dan wata buƙata.
- Kasuwanci na haram koda girmansa ya yawaita; to shi abin cirewa albarka ne babu alheri a cikinsa.
- AlƘari ya ce: Tafiyar albarkar abin kasuwanci; kodai dan lalacewa ne wanda zai riske shi a cikin dukiyarsa, ko dan ciyar da shi a abinda anfaninsa ba zai koma zuwa gare shi ba a nan duniya ko ladansa a nan gaba (lahira), ko ya wanzu a wurinsa kuma a haramta masa anfaninsa, ko wanda ba zai gode masa ba ya gaje Shi.
- Annawawi ya ce: A cikinsa akwai hani akan yawan rantsuwa a cikin ciniki, domin rantsuwa ba tare da wata buƙata ba abin ƙi ce, kuma zai haɗa da yawaitar haja gare shi, wataƙila mai siye ya ruɗu da rantsuwar.
- Yawan rantsuwa tawaya ne a imani, kuma tawaya ne a cikin Tauhidi; domin cewa yawan rantsuwa yana kaiwa zuwa abubuwa biyu: Na farkonsu: Sakaci a cikin hakan da rashin kulawa, al'amari na biyu: Ƙarya, domin cewa duk wanda rantsuwarsa ta yawaita zai afka cikin ƙarya, to ƙaranta hakan yana kamata da kuma rashin yawaita rantsuwa, saboda haka ne tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Ku kiyaye rantse-rantsenku} [al-Ma'idah: 89].