- Shiga aljanna yana da sabubban da suka rataya da Allah - Maɗaukakin sarki, daga cikinsu akwai: Tsoronsa, da kuma sabubban da suke rataya da mutane, daga cikinsu akwai: Kyawawan ɗabi'u.
- Hatsarin harshe ga mai shi, kuma yana daga sabubban shiga wuta.
- Hatsarin sha'awe-sha'awe da ayyukan alfasha ga mutum, kuma suna daga mafi yawan sabubban shiga wuta.