/ Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa cikar kyawawan ɗabi’u, yana da wannan rigayar a dukkanin kyawawan ɗabi’u, kamar kyakkyawar magana, bayar da kyauta, sakin fuska, rashin cutarwa, juriyarsa ga mutane.

Hadeeth benefits

  1. Cikar ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
  2. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne babban abin koyi a kyawawan ɗabi’u.
  3. Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kyawawan ɗabi’u.