- Nawawi ya ce: Wannan ka'ida ce tabbatacciya a shari'a, ita ce: cewa abinda ya kasance daga babin giramamawa da daukaka, kamar sanya tufa da wanduna da huffi da shiga masallaci da asuwaki da sanya kwalli, da yanke farce, da rage gashin baki, da taje kai shi ne yi masa kum, da cire gashin hammata, da aske kai, da sallama daga sallah, da wanke gabban alwala, da fita daga bandaki, da ci da sha, da musafaha, da sumbatar (Alhajarul Aswad) bakin dutse, da wanin hakan na abinda yake a cikin ma'anarsa anso damantawa a cikinsa.
- Amma abinda ya kasance kishiyarsa kamar shiga bandaki, da fita daga masallaci da face majina, da tsarki, da tube tufafi da wanduna da huffi da abinda ke kama da hakan, to an so haguntawa a cikinsa, wannan saboda girmama dama da kuma daukakarta.
- "Damantawa yana kayatar da shi". Ya kunshi: Farawa a cikin ayyuka da hannun dama, da kafar dama, da bangaren dama, da bada abu da dama.
- Nawawi ya ce: Ka sani cewa daga gabban alwala a kwai wadanda ba’a son damantawa a cikinsu; shi ne kunnuwa da tafuka da kundukuki kai za'a tsarkakesu ne karo daya, idan hakan ya wuyata kamar a hakkin mai dungu da makamancinsa; sai a gabatar da dama.