Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe,...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba da labari game da kalmomi biyu da mutum zai furta su ba tare da wahala ba, kuma akowane h...
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga...
Ma’aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda a rana ya faɗa sau ɗari: Tsarki ya tabbata ga Allah haɗi da go...
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga All...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labari cewa anbaton Allah (Zikiri) da waɗannan kalmomi masu girma, shi ya fi duniya da...
Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Mafificin zikiri: Babu abin bau...
Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa mafificin zikiri: "La ilaha illal lahu" Ma'anarta babu abin bautawa da gaski...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: In ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, Godiya ta tabbata ga Allah, Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Allah ne mafi girma.
Fadin haka ya fi min duk abin da rana ta fito a kansa.
Daga Jabir -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: "Mafificin zikiri: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma mafificiyar addu'a: Godiya ta tabbata ga Allah".
Daga Khaulah ’Yar Hakim Al-Sulamiyyah, ta ce: Na ji Ma’aikin Allh tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin.
Daga Abu Humaid ko daga Abu Usaid ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan mutum zai shiga gidansa, sai ya ambaci sunan Allah a yayin shigarsa da lokacin cin abincin sa , Shaidan zai ce : Babu makwanci gareku, kuma babu abincin dare, idan zai shiga bai ambaci sunan Allah a yayin shigarsa ba, Shaidan zai ce: Kun sami makwanci, idan bai ambaci Allah a lokacin cin abincin sa ba, zai ce : Kun riski makwanci da abincin dare".