Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Kalmomi guda biyu masu sauƙi a harshe, masu nauyi a ma'auni, masu soyuwa ga Ubangiji Al-Rahman: Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba da labari game da kalmomi biyu da mutum zai furta su ba tare da wahala ba, kuma akowane hali, kuma ladansu mai girma ne a ma'auni, kuma Ubangijimmu Al-Rahman - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - Yana sonsu:
Tsarki ya tabbata ga Allah Mai girma, tsarki ya tabbata ga Allah da godiya a gareshi; saboda abin da suka ƙunsa na siffanta Allah da girma da cika, da tsarkakeshi daga tawaya - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
Hadeeth benefits
Mafi girman zikiri shi ne a haɗa tsakanin tsarkakeshi da yabo gareshi a cikinsa.
Bayanin yalwar rahamar Allah ga bayinsa, Yana sakayya da gwaggwaɓan lada a kan aiki kaɗan.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others