Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imta...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'a da ni'ima da farin ciki da kyau a duniya, kuma Allah Ya isar da shi zuwa ni'imar a...
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar da wanda ya nemi ilimi dan yi wa malamai alfahari, da bayyanar da cewa ni malami ne...
Daga Usman Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce: "Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alku...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin mafi falalar Musulmai, wanda kuma yake ƙololuwar daraja a wurin Allah shi ne, w...
Daga Abu Abdurrahman Al-Sulami - Allah ya yi masa rahama - ya ce: Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Alla...
Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna koyo daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayoyi goma daga Alkur’ani, b...
An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labari cewa kowanne Musulmi ne ya karanta harafi daga littafin Allah, to, yana da lada a...

Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa: "Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa malamai alfahari da shi, ko ku yi musu da wawaye da shi, kuma kada ku nufi bijiro da shi a zababbun majalisai, wanda ya aikata haka to wuta wuta".

Daga Usman Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi ya ce: "Mafi alherinku shi ne wanda ya koyi Alkur’ani kuma ya koyar da shi".

Daga Abu Abdurrahman Al-Sulami - Allah ya yi masa rahama - ya ce: Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zantar damu cewa su sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki, suka ce: Sai muka koyi ilimi da aiki.

An karbo daga Abdullahi Ɗan Mas’ud Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya karanta wani harafi daga littafin Allah, to, yana da lada, kuma kowane lada za a ninkashi goma. amma ba zan ce Alif Laam Meem harafi ɗaya ba ne, sai dai Alif, harafi ne, Laam harafi ne, Meem harafi ne"

Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin dayanku yana son idan ya koma zuwa iyalansa ya samu manyan taguwowi masu ciki masu giba?" muka ce: Eh. Ya ce; "To ayoyi uku dayanku zai karantasu a cikin sallarsa sun fiye masa alheri daga taguwowi uku manya masu ciki".

Daga Abu Musa Al-ash'ariy Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ku dinga maimaita wannan Alƙur’anin, ina rantse muku da wanda ran Muhammad yake a hannunSa ya fi saurin kufcewa sama da raƙumin da ya ke a dabaibayi.

Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".

Daga Ubayyu Dan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya kai baban Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare da kai?" ya ce: Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Ya ce: "Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir".

Daga Abu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wanda ya karanta ayoyi biyu na ƙarshen Suratul Bakara da daddare sun ishe shi.

Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf".