- Ana so a yawaita ibada da Sallolin Nafila a gidaje.
- Ba ya halatta yin Sallah a maƙabarta, domin hakan hanya ce daga hanyoyin shirka da wuce iyaka ga masu su, in banda sallar Janaza.
- Hanin yin Sallah a inda akwai kabari, ya tabbata a wurin Sahabbai, saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana a sanya gidaje kamar maƙabartu, waɗanda su ba a Sallah a cikinsu.