- Bayanin falalar Suratul Kahf, kuma cewa (ayoyin) farkonta ko (ayoyin) ƙarshenta suna kiyayewa daga fitinar Dajjal.
- Labartawa daga al'amarin Dajjal, da bayanin abinda zai tsare shi .
- Kwaɗaitarwa akan haddace Suratul Kahf cikakkiya, idan ya gajiya to ya haddace ayoyi goman farko da na ƙarshe.
- AlƘurɗubi ya faɗa a cikin sababin hakan: An ce: Dan abinda ke cikin ƙissar Ashabul Kahf (Ma’abota Kogo) na abubuwan mamaki da ayoyi, wanda ya tsaya a kan su ba zai yi mamakin al'amarin Dajjal ba kuma hakan ba zai shagaltar da shi ba to ba zai fitinu da shi ba, kuma an ce: Saboda faɗinSa ne - Maɗaukakin sarki -: {Domin ya yi gargaɗi da azaba mai tsanani daga gare shi } dan yin riƙo da keɓantar azaba da tsanani daga gare shi , shi ya dace da abinda zai kasance daga Dajjal na da'awar Uluhiyya (allantaka) da rinjayarsa da girman fitinarsa, saboda haka ne tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya girmama al'amarinsa kuma ya gargaɗar daga fitinarsa, sai ma'anar hadisin ta zama: Cewa wanda ya karanta wadannan ayoyin kuma ya yi nazarin ma'anoninsu kuma ya tsaya akaan ma'anoninsu to ya kuɓuta daga gare shi .