Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa yiwu...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa dukkanin ayyuka ababen izina ne da niyya, wannan hukuncin mai gamewa ne a ci...
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga al'...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya yi kirkira a Addini ko ya aikata wani aikin da wani dalili bai yi nu...
Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayi...
Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - yana ba da labari cewa Jibril - aminci ya tabbata a gare shi - ya fito wurin sahabbai - Allah Ya yarda da s...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "An gina musulunci abisa a...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar...
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bay...

Daga Umar dan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira daa mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyya, kaɗai mutum (ana bashi ladan) abin da ya niyyata ne, wanda hijirarsa ta kasance zuwa ga Allah da manzonsa, to, hijirarsa tana ga Allah da manzonsa, wanda hijirarsa ta kasance don duniya da zai sameta, ko wata mace da zai aureta, to, hijirarsa tana ga abin da ya yi hijira zuwa gareshi". A wani lafazin na Bukhari; "Dukkan ayyuka (ba sa yiwuwa) sai da niyyoyi, kaɗai kowane mutum (ana ba shi ladan) abin da ya niyyata ne".

Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya farar da (wani abu) daga al'amarinmu wannan abinda ba ya ciknsa to an mayar masa". Daga Muslim: "Wanda ya aikata wani aiki wanda ba ya kan al'amarinmu to shi abin an mayar masa".

Daga Umar ɗan khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata rana muna zaune a wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da wani mutum ya ɓullo mana mai tsananin farin tufafi, mai tsananin baƙin gashi, ba a ganin gurbin tafiya a gareshi, kuma wani daga cikinmu bai sanshi ba, har ya zauna zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya jingina gwiwoyinsa zuwa gwiwoyinsa, ya ɗora tafukansa a kan cinyoyinsa, sai ya ce: Ya Muhammad, ba ni labari game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Muslulunci: shi ne ka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa (Annabi) Muhammad manzon Allah ne, ka tsai da sallah, ka ba da zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci ɗakin (Allah) idan kana da ikon tafiya zuwa gareshi" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: Sai muka yi mamakinsa, yana tambayarsa yana gasgatashi, ya ce: Ka ba ni labari game da imani, ya ce: "Ka ba da gaskiya da Allah, da mala'ikunsa, da littattafansa, da manzanninsa, da ranar lahira, ka ba da gaskiya da kaddara alherinta da sharrinta" ya ce: ka yi gaskiya, ya ce: ka ba ni labari game da kyautayi, ya ce: "Ka bautawa Allah kamar kai kana ganinsa, idan ka kasance ba ka ganinsa, to, shi yana ganinka" Ya ce: ka ba ni labari game da al-ƙiyama, ya ce: Wanda ake tambayar bai fi wanda yake tambayar sani ba". Ya ce: Ka ba ni labarin alamominta, ya ce: "Kuyanga za ta haifi uwargijiyarta, kuma za ka ga marasa takalma talakawa masu kiwon dabbobi suna gasar tsawaita gidaje" Ya ce: Sannan ya tafi, sai na zauna ɗan wani lokaci sannan ya ce da ni: "Ya Umar, shin ka san waye mai tambayar?" Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "To, lallai Jibrilu ne ya zo muku don ya sanar da ku addininku".

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "An gina musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".

Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki. Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.

Daga Tarik Ɗan Ashyam al’Ashja’i, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi yana cewa: Duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ya kuma kafircewa abin da ake bautawa koma bayan Allah, to, dukiyarsa da jininsa sun haramta, hisabinsa kuma yana ga Allah.

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, wadanne abu biyu ne masu wajabtawa? Sai ya ce: "Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna, wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta"

Daga Abdullahi Dan Mas'ud - Allah ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fadi wata kalma ni kuma na fadi wata daban, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wanda ya mutu alhali shi yana kiran kishiya wanin Allah zai shiga wuta" Ni kuma na ce: Wanda ya mutu alhali shi ba ya kiran kishiya ga Allah zai shiga aljanna.

Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce wa Mu'azu Dan Jabal, lokacin da ya aike shi zuwa Yaman: "Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, idan su sun bika a kan hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu salloli biyar a kowanne yini da dare, idan su sun bika da hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu sadaka da za'a karba daga mawadatan su sai a dawo da ita ga talakawansu, idan su sun bika da hakan, to na haneka da manyan dukiyoyin su, ka tsoraci addu'ar wanda aka zalinta, lallai cewa ita babu wani shamaki tsakanin ta da Allah".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce ya Manzon Allah waye mafi azirtar mutane da cetanka a ranar Kiyama? Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Hakika ya Abu Huraira na yi zatan babu daya da zai tambayeni game da wannan hadisin na farko daga kai, saboda abinda na gani na kwadayinka akan hadisi, mafi arzikin mutane da cetona a ranar Kiyama, wanda ya ce babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, yana mai tsarkakewa daga zuciyarsa ko ransa".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.