Daga Nu'umanu dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : - sai Nu'uman...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana wata ƙa'ida mai gamewa game da abubuwa, cewa sun kasu a shari'a zuwa kashi uku: B...
Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku zagi sahabbaina...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana hani daga zagin sahabbai, musamman ma marigaya na farko daga muhajirai da mutanen Madina;...
Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce:...
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - yana ba da labarin cewa ya kasance yana ƙarami yana haye tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare...
Daga Sufyan Dan Abdullah AlSakafi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi wanink...
Sahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata mag...
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a s...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana wajaba halin musulmai sashinsu tare da sashi ya zama da son alheri da taus...

Daga Nu'umanu dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa : - sai Nu'uman ya sakko da 'yan yatsunsa zuwa kunnuwansa -: "Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".

Daga Abu Sa'id AlKhudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa".

Daga ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na kasance a bayan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wata rana, sai ya ce: "Ya kai yaro, zan sanar da kai wasu kalmomi, ka kiyaye Allah Zai kiyayeka, ka kiyaye Allah zaka sameshi a daura da kai, idan za ka yi roƙo, to, ka roƙi Allah, idan za ka nemi taimako, to, ka nemi taimakon Allah, ka sani cewa da al'umma za su taru a kan su amfaneka da wani abu, ba za su amfaneka ba sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta maka, da za su taru a kan su cutar da kai da wani abu, ba za su cutar da kai ba, sai da abin da tabbas Allah Ya rubuta a kanka, an ɗauke alƙaluma kuma takardu sun bushe".

Daga Sufyan Dan Abdullah AlSakafi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".

Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".

Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah, mu muna tafiya a teku, kuma muna ɗaukar ruwa kaɗan tare da mu, idan muka yi alwala da shi zamu ji ƙishirwa, shin zamu yi alwala daga ruwan kogi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne".

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ruwa da abinda yake zuwa masa na dabbobi da zakokai, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa".

Daga Abu Ayyuba Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma" Abu Ayyub ya ce: Sai muka je Sham sai muka samu banɗakuna an gina su ɓangaren alƙibla sai mu juya, muka nemi gafarar Allah - Maɗaukakin sarki -".

Daga Abu Katada - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa".

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu.