Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa daga sharuddan ingancin sallah: Tsarki, to yana wajaba akan wanda ya yi nufi...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Umar Dan Alkhaddab ya bani labari: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan...
Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya gama alwalarsa, sai ya...
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa M...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi tafiya daga Makka zuwa Madina a tare da shi akwai sahabbansa, sai suka samu ruwa a hanyar...
Daga Amr ɗan Amir daga Anas ɗan Malik ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah,...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a kowacce sallar farilla ko da alwalarsa ba ta karye ba, hakan don tabb...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a sashin lokutansa idan zai yi alwala sai ya wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalar...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba ya karbar sallar dayanku idan ya yi hadasi har sai ya yi alwala"
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Umar Dan Alkhaddab ya bani labari: Cewa wani mutum ya yi alwala, sai ya bar tabo (Lam’a) gurin farce a kan ƙafafunsa, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gan shi (wurin) sai ya ce: "Koma ka kyautata alwalarka" Sai ya dawo, sannan ya yi sallah.
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Mun dawo tare da manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga Makka zuwa Madina har sai da muka kasance a wani ruwa a hanya, sai wasu mutane suka yi gaggawar (sallar) La'asar, sai suka yi alwala alhali suna gaggawa, sai muka kai gare su alhali karshen kafafuwanusu suna haske (lam’a) ruwa bai tabasu ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azaba ta wuta ta tabbata ga karshen kafa ku cika alwala".
Daga Amr ɗan Amir daga Anas ɗan Malik ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah, sai na ce: Yaya kuka kasance kuna aikatawa? sai ya ce: Alwala tana isar ɗayanmu muddin dai bai yi kari (hadasi) ba.
Daga Humran bararran bawa na Usman Dan Affan cewa ya ga Usman Dan Affan ya nemi da akawo masa ruwan alwala, sai ya karkato da kwaryar (butar Alwala), sai ya wankesu sau uku, sannan ya shigar da (hannunsa na) dama a ruwan alwalar, sannan ya kuskure baki ya shaƙa ruwa ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau uku, da hannayensa zuwa gwiwar hannaye sau uku, sannan ya shafi kansa, sannan ya wanke kowacce ƙafa sau uku, sannan ya ce: Na ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - ya yi alwala irin wannan alwalar tawa, sai ya ce: "Wanda ya yi alwala irin wannan alwalar tawa sannan ya yi sallah raka'a biyu bai zantar da ransa a cikinsu ba, to, Allah Zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubinsa".
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan dayanku zai yi alwala to ya sanya ruwa a hancinsa sannan ya face, wanda zai yi tsarkin hoge to ya yi shi wutiri, idan dayanku ya farka daga baccinsa to ya wanke hannunsa kafin ya shigar da su a ruwan alwalarsa, domin cewa dayanku ba ya sanin a'ina hannunsa ya kasance". Lafazin Muslim: "Idan dayanku ya farka daga baccinsa kada ya nutsa hannunsa a cikin kwarya har sai ya wankesu sau uku, domin cewa shi ba ya sanin a'ina hannunsa ya sakance ".
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata".
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya fito daga bayan gida yana cewa: "Ina neman gafararKa".
Daga Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yace: "Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".