Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Buhari ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a sashin lokutansa idan zai yi alwala sai ya wanke kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau ɗaiɗai, sai ya wanke fuska - daga [cikin wanke fuska] akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau ɗaiɗai, wannan shi ne gwargwadon wajibi.
Hadeeth benefits
Wajibi a wanke gaɓɓai (shi ne) sau ɗaiɗai, abin da ya ƙaru, to, mustahabbi ne.
Halaccin yin alwala sau ɗaiɗai a wasu lokuta
Abin shar'anta wa a shafar kai (shi ne) sau ɗaiɗai.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others