- An so faɗin: "Ina neman gafafarKa" bayan fitowa daga wurin biyan buƙata.
- Neman gafarar da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi ga Ubangijinsa a dukkanin halaye.
- An ce: A cikin sababin neman gafara bayan biyan buƙata: Don taƙaitawa ne a cikin godiyar ni'imomin Allah masu yawa , daga cikinsu akwai sawwaƙa fitar abinda yake cutarwa, kuma ina neman gafararKa dan na shagalta daga anbatanKa a lokacin biyan buƙata.