Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah
Daga Amr ɗan Amir daga Anas ɗan Malik ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah, sai na ce: Yaya kuka kasance kuna aikatawa? sai ya ce: Alwala tana isar ɗayanmu muddin dai bai yi kari (hadasi) ba.
Buhari ne ya rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a kowacce sallar farilla ko da alwalarsa ba ta karye ba, hakan don tabbatar da lada da kuma falala.
Ya halatta ya sallaci sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya muddin dai yana da alwala.
Hadeeth benefits
Mafi yawancin aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne yin alwala ga kowace sallah; don neman mafi cika.
An so yin alwala a lokacin kowace sallah.
Halaccin yin sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others