Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku ji tsoron zalunci, domin zalu...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga zalinci. Daga cikin Nau’ukansa akwai: Zalintar mutane da zalintar kai, da za...
Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, ha...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan cewa ci gaba da zalunci da laifuka da shirka da zaluntar mutane a haƙƙoƙinsu...
Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa...
Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya za...
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce:...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa...
Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - Lallai wasu mutane daga mushrikai, sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun yi zina sun yawaita, sai suka zo w...
Wasu mutane daga mushrikai sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun kasance haƙiƙa sun yawaita kisa da zina, sai suka cew...

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku, har ya kaisu sun zubar da jininsu, suka halarta abinda aka haramta musu".

Daga Abu Musa Allah Ya yarda da shi ya ce: Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.

Daga Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - ya ce: Ya ce: "Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya".

Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - Lallai wasu mutane daga mushrikai, sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun yi zina sun yawaita, sai suka zo wa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai suka ce: Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata, sai (faɗin Allah) ya sauka: {Waɗanda ba sa kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba sa kashe rai wanda Allah Ya haramta face da haƙƙi, kuma ba sa yin zina} [Al-Furqan: 68], kuma (wannan ayar) ta sauka: {Kace: (Allah Ya ce), "Ya ku bayiNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukanku! kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah} [Al-Zumar: 53].

Daga Hakim Dan Hizam - Allah Ya yarda da shi - ya ce:: Na ce: Ya Manzon Allah, kana ganin abubuwan da nake ibada da su a lokacin Jahiliyya na sadaka ko 'yantawa, da sada zumunci, shin a akwai lada? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a agre shi - ya ce: "Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri".

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".

Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - ya ce:Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa, Ya kai ɗan Adam da zunubanka sun kai ƙololuwar sama sannan ka nemi gafarata zan gafarta maka, babu ruwaNa, Ya kai ɗan Adam lallai cewa kai da ka zo min da kurakurai cikin ƙasa sannan ka gamu dani ba yi min tarayya da wani abu ba, da na zo maka da gafara cikinta".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi -, a cikin abin da yake hakaitowa daga Ubanngijinsa - mai girma da ɗaukaka -, ya ce: "Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, sai (allah) Mai girma da ɗaukaka ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma yana yin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo ya sake yin zunubi, sai yace: Ya Ubangiji Ka gafarta min, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, kuma Yanayin uƙuba a kan zunubi, sannan ya dawo sai yayi zunubin, sai ya ce: Ya Ubangiji ka gafarta min laifina, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: Bawana ya yi laifi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta zunubi, kuma yanayin uƙuba a kan zunubi, ka aikata abin da ka so haƙiƙa na gafarta maka".

Daga Aliyu Allah ya yarda da shi ya ce: Ni na kasance mutum ne idan na ji wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Zai anfanar da ni daga abinda Ya so daga gare shi, Ya anfanar da ni da shi, idan wani mutum daga sahabbansa ya zantar da ni zan sa shi ya rantse, idan ya rantse mini sai in gasgata shi, cewa Abubakar Allah ya yarda da shi ya zantar da ni, kuma Abubakar ya yi gaskiya, ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum da zai aikata laifi, sannan ya tashi ya yi alwala, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, sai Allah Ya gafarta masa", sannan ya karanta wannan ayar: {Sune wadanda idan sun aikata wata alfasha ko sun zalinci kansu sai su tuna Allah sai su nemi gafarar zunubansu ga (Allah)}. [Aal-Imran: 135].

Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta".

Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura yana cewa: Wa zai roƙeni in amsa masa,?? wa zai tambaye ni in ba shi, ?? wa zai nemi gafarata in gafarta masa ??