Bayani
Annabi -tsira da amincin Allah su tabbat a gareshi - yana ruwaitowa daga Ubangijinsa cewa idan bawa ya aikata zunubi sannan ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina, Allah - Maɗaukakin sarki - Zai ce: Bawana ya aikata zunubi, kuma ya san cewa yana da Ubangijin da zai gafarta masa zunubi, Ya suturtashi ya yafe masa, ko yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafarta masa. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Ya yi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana. Sannan bawan ya dawo sai ya yi zunubi, sai ya ce: Ya Ubangiji Ka gafarta min zunubina, sai Allah Ya ce: Bawana ya aikata zunubi, sai ya san cewa yana da Ubangijin da yake gafarta zunubi, sai ya suturta shi ya yafe masa, ko Yayi masa uƙuba a kansa, haƙiƙa Na gafartawa bawana, sai ya aikata abin da ya so muddin dai cewa shi a duk lokacin da ya yi zunubi zai bar zunubin ya yi nadama, ya yi niyyar barin komawa a cikinsa, sai dai zuciyarsa tana rinjayarsa, sai ya afka a cikin zunubi karo na gaba, muddin dai yana aikata haka yana zunubi yana tuba, to, zan gafarta masa; domin cewa tuba yana rushe abin da ke kafinsa.