- Yalwar rahamar Allah - Maɗaukakin sarki - da gafararSa da falalarSa.
- Falalar Tauhidi, kuma cewa Allah Yana gafarta zunubai da sabo ga masu tauhidi.
- Haɗarin shirka kuma cewa Allah ba Ya gafara ga masu shirka.
- Ibnu Rajab ya ce: Haƙiƙa wannan Hadisin ya ƙunshi sabubba uku waɗanda gafarta zunubai suke samuwa da su: Na farko: Addu'a tare da ƙauna. Na biyu: Istgfari da neman tuba. Na uku: Mutuwa akan tauhidi.
- Wannan Hadisin yana daga abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yake ruwaito shi daga Ubangijinsa, ana ambatonsa da Hadisi Ƙudsi, ko Ilahi, shi ne wanda lafazinsa da ma'anarsa daga Allah ne, sai dai shi babu keɓance-keɓancen Alƙur’ani a cikinsa waɗanda ya keɓanta da su daga waninsa, kamar bauta da karanta shi, da yin alwala sabo da taba shi da fito na fito(ƙalubalanta) da gajiyarwa, (Mu’ujiza) da sauransu.
- Zunubai nau'i uku ne: Na farko: Shirka da Allah; wannan Allah ba Ya gafarta shi, Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya ce: {Lallai cewa shi wanda ya yi shirka da Allah to haƙiƙa Allah Ya haramta masa aljanna}.
- Na biyu: Zalintar bawa ga kansa a cikin abinda ke tsakaninsa da tsakanin Ubangijinsa na zunubai da sabo; domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - zai gafarta hakan, kuma zai ƙetare in Ya so.
- Na uku: Zunuban da Allah baYa barin komai daga garesu; su ne zalintar bayi sashinsu da sashi, babu makawa daga sakayya.