- Falalar musulunci da girmansa kuma cewa shi yana rusa abin da ya gabata na zunubai.
- Yalwar rahamar Allah ga bayinSa da gafararSa da rangwaminSa.
- Haramcin shirka, da haramcin kashe rai ba tare da wani haƙƙi ba, da haramcin zina, da narko a kan wanda ya aikata waɗannan zunuban.
- Tuba na gaskiya abin wanda ya hadu da ikhlasi da aiki na gari yana kankare dukkanin manyan zunubai har ma da kafircewa Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Haramcin yanke ƙauna daga rahamar Allah - tsarki ya tabbatar maSa -.