- Karɓar tuba yana nan muddin ƙofar na nan a buɗe, kuma ana kulle ƙofarta ne da ɓullowar rana daga mafaɗarta.
- Kuma idan mutum ya tuba kafin gargarar mutuwa, shi ne rai ya kai maƙogwaro.
- Rashin yanke ƙauna saboda zunubi, domin cewa afuwar Allah - tsarki ya tabbatar maSa - da rahamarSa masu yalwa ne, kuma ƙofar tuba abuɗe take.
- Sharuɗɗan tuba: Na ɗaya: Barin aikata laifin. Na biyu: Nadama akan aikata shi. Na uku: Kudirce niyya akan ba zai koma zuwa gare shi ba har abada.
- Wannan idan ya kasance a cikin haƙƙoƙin Allah - Maɗaukakin sarki - ne, idan ya kasance ya rataya da haƙƙin wani daga haƙƙoƙin bayi, to an sharɗanta ga ingancin tuban ya mayar da wannan haƙƙin ga mai shi, ko mai haƙƙin ya yi masa afuwa.