Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bak...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance lokuta da yawa yana yin asuwaki kuma yana umarni da a yi shi, hakan yana karfafuwa a...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa shi da ba dan tsoron wahala ga muminai daga al'ummarsa ba da ya wajabta mu...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wajibi ne a kan kowanne musulm...
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa wajibi ne mai ƙarfi a kan kowanne musulmi baligi mai hankali ya yi...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Dabi'a (ta addinin M...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni:
Na farkonsu: Ka...
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira da amincin Allah...
Aliyu Dan Abu Dalib - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa ya kasance da yawan maziyyi yana fita daga gare shi - shi wani ruwa ne fari siriri...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata".
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance mutum ne mai yawan maziyyi, na kasance ina jin kunyar tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda matsayin 'yarsa sai na umarci Mikdad Dan Aswad sai ya tambaye shi sai ya ce: "Ya wanke gabansa ya yi alwala". Ga Bukhari: Sai ya ce: "Ka yi alwala ka wanke gabanka".
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi wankan janaba, sai ya wanke hannayensa, ya yi alwala alwalarsa domin sallah, sannan ya yi wanka, sannan ya tsettsefe gashinsa da hannunsa har sai ya tabbar cewa ya jika fatarsa, sai ya zuba ruwa akansa sau uku, sannan ya wanke ragowar jijkinsa. Ta ce: Na kasance ina wanka ni da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - daga kwarya daya muna kanfatowa daga gareta gaba daya.
Daga Ammar dan Yasir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aikeni wata bukata, sai na samu janaba ban samu ruwa ba, sai na tumurmusa a bigire kamar yadda dabba take tumurmusa , sannan na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai na ambata masa hakan sai ya ce: "Kadai ya isheka ka aikata kamar haka da hannayenka" sannan ya bugi kasa bugu daya da hannayensa, sannan ya shafi hagu akan dama, da bayan tafukansa da kuma fuskarsa.
Daga Mugira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a wata tafiya, sai na sunkuyo don in cire masa huffi, sai ya ce: "Ka barsu don na shigar da su suna da tsarki" sai ya yi shafa akansu.
Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce : Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ɗayanku ya ji wani abu a cikinsa, sai ya rikitar da shi cewa shin wani abu ya fita daga gare shi ko a'a, to, kada ya fita daga masallaci har sai ya ji kara ko ya ji waji wari".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai".
Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".