- Wanka (Wankan tsarki) nau'i biyu ne: Mai isarwa da kuma cikakke, amma mai isarwa sai mutum ya yi niyyar tsarki, sannan ya game jikinsa da ruwa tare da kuskurar baki da shaka ruwa.
- Amma cikakken wanka sai ya yi wanka kamar yadda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wanka a wannan hadisin.
- Ana anfani da lafazin janaba ga dukkanin wanda ya fitar da maniyyi, ko ya tara da matarsa koda bai yi maniyyi ba.
- Halaccin kallon daya daga ma'aurata al'aurar dayan, da kuma wankansu daga kwarya daya.