- Yawun kare najasa ne najasa mai kauri.
- Lallagin kare a cikin kwarya yana maida ita mai najasa, kuma yana najasantar da ruwan dake cikinta.
- Tsarkakewa da turbaya da maimaitawa sau bakwai ya kebanci tsarkakewa ne daga lallaginsa banda fitsarinsa da bayan gidansa, da ragowar abinda kare ya bata shi .
- Yadda wanke kwarya da turbaya: A sanya ruwa a cikin kwarya sai a zuba turbaya (kasa) a ciki, sannan a wanke kwarya da wannan cuɗaɗɗen.
- Zahirin Hadisin mai gamewa ne a dukkanin karnuka, har karnukan da shari’a ta bada iznin a dauke su, misalin karnukan farauta da na gadi da na kiwo.
- Sabulu da makilin ba sa tsayawa a matsayin turbaya; domin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nassanta turbaya ne.