- Wajabcin wanka akan mace a yayin karewar kwanukan al’adarta.
- Wajabcin sallah akan mai jinin cuta.
- Haila: Jini ne na dabi'a da mahaifa take turo shi ta gaban mace baliga, da yake samunta a wasu kwanuka sanannu.
- Jinin cuta: Zubar jini ba'a lokacinsa ba daga kasan mahaifa ba daga can cikin mahaifa ba.
- Banbanci tsakanin jinin haila da jinin cuta: Cewa jinin haila baki ne mai kauri mai wari, amma jinin cuta to shi jane siriri ba shi da wari.