- Karfafuwar halaccin asuwaki bayan baccin dare, hakan domin barci yana hukunta canzawar bashin baki ne, shi kuma asuwaki shi ne kayan tsaftace shi.
- Karfafuwar halaccin asuwaki a lokacin canjawar bashi a baki, dan yin riko da ma'anar data gabata.
- Shar’antuwar tsafta ta fuskar gamewa, kuma ita tana daga sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma tana daga manyan ladubba.
- Yin asuwaki a baki gabaɗayansa ya kunshi: Hakora, da dadashi, da harshe.
- Asuwaki shi ne itacen da ake yanko shi daga bishiyar kirya ko waninta, ana anfani da shi a tsaftace baki da hakora, kuma yana daɗaɗa baki, yana gusar da warin da ba'a so.