Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sallaci sanya...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zaburar da kwaɗaitarwa akan sallar sanyaya biyu ; su ne sallar asuba da la'asar, kuma Ya yi...
Daga Jundub ɗan Abbdullah AL Qasri- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya sall...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya sallaci Asuba, to, zai kasance cikin kiyayewar Allah da gadins...
Daga Abu Buraidah Ɗan Husaib, Allah ya yarda da shi ya ce: Ku gaggauta sallar La’asar a kan lokaci, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a g...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya tsawatar a kan jinkirta sallar La’asar daga lokacinta da gangan, kuma duk wanda ya yi hakan, to...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallace...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i...

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna".

Daga Jundub ɗan Abbdullah AL Qasri- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya sallaci sallar Asuba, to, zai kasance cikin alƙawarin Allah, Kada ku kuskura Allah Ya kamaku da wani (laifi) cikin alƙawarinsa; domin cewa duk wanda ya nemeshi da wani abu (na laifi) Zai kamashi, sannan Ya kifar da shi ta fuskarsa a cikin wutar Jahannama".

Daga Abu Buraidah Ɗan Husaib, Allah ya yarda da shi ya ce: Ku gaggauta sallar La’asar a kan lokaci, domin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Duk wanda ya bar sallar la’asar, to, aikinshi ya ɓaci.

Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".

Daga Ibnu Abi Aufa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Allah Ubangijimmu godiya ta tabbata gareKa, cikar sammai da cikar ƙasa da cikar abin da ka so daga wani abu bayan nan"

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'.

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.

Daga Hiɗɗan ɗan Abdullahi Al-Raƙashi ya ce: Na sallaci wata sallah tare da Abu Musa Al-Assh'ari, a lokacin zama sai wani mutum daga mutane ya ce: An haɗa sallah da aikin alheri da kuma zakka, ya ce: Lokacin da Abu Musa ya gama sallar ya yi sallama, sai ya juya ya ce: Waye mai faɗin kalmar kaza da kaza a cikinku? ya ce: Sai mutane suka yi shiru, sannan ya ce: Waye ya faɗi kalmar kaza da kaza a cikinku? sai mutane suka yi shiru, sai ya ce: Wataƙila kai Hiɗɗanu kai ka faɗeta? sai ya ce: Ban faɗeta ba, haƙiƙa na ji tsoron kada ka zargeni da ita, sai wani mutum daga mutanen ya ce: Ni na faɗeta, kuma ban nufi komai da ita ba sai alheri, sai Abu Musa ya ce: Shin kun san me zaku fada a sallarku? lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana huɗuba sai ya bayyana mana sunnonimmu, ya kuma sanar da mu sallolinmu. "Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara, idan ya ce: {Ba waɗanda ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba} [Al-Fatiha: 7], sai ku ce: Ameen, Allah zai amsa muku, idan ya yi kabbara ya yi ruku'u, sai ku yi kabbara ku yi ruku'u, domin cewa liman yana yin ruku'u ne kafinku, kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sai ku ce: Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa, Allah Zai jiye muku (wato Zai amsa); domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya faɗa a kan harshen AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, idan ya yi kabbara ya yi sujjada sai ku yi kabbara sai ku yi sujjada, domin cewa liman yana yin sujjada ne kafinku kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan an zo wurin zama; to, farkon abin da ɗayanku zai faɗa (shi ne): gaisuwa ta tabbata ga Allah tsarkakan salloli sun tabbata ga Allah, aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da bayin Allah nagari, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina shaida cewa (Annabi) muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne".

Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani : "(Tsarkakan) Gaisuwa ta tabbata ga Allah, da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agareka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne". Acikin wani lafazi na su: "Lallai cewa Allah Shi ne aminci, idan dayanku ya zauna a cikin sallah to ya ce: (Tarakakan) Gaisuwa sun tabbata ga Allah da salloli da tsarkake-tsarkake, aminci ya tabbata agreka Ya kai wannan Annabi da rahamar Allah daalbarkarSa, aminci ya tabbata agaremu da bayin Allah na gari. Idan ya fadeta za ta samu kowanne bawan Allah nagari a sama da kasa, ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonsa ne, sannan ya zabi abin yake so ya roka".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).

Daga Ma’adan ɗan Abu Dalha Al-Ya'amury ya ce: Na gamu da Sauban 'yantaccen bawan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai na ce: Ka ba ni labari da wani aikin da zan aikata shi Allah Ya shigar da ni Aljanna da shi? ko ya ce, na ce: Da mafi son ayyuka zuwa ga Allah, sai ya yi shiru. Sannan na tambaye shi, sai ya yi shiru, sannan na tambaye shi a karo na uku sai ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da wannan, sai ya ce: "Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin kai ba za ka yi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure da ita" Ma'adan ya ce: Sannan na gamu da Abu al-Darda'i sai na tambaye shi sai ya fada min abinda Sauban ya faɗa mini.