Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ci...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin Allah maɗaukakin sarki Ya ce: Ya kai Ɗan Adam ka ciyar cikin ciyarwar wajibi da...
Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai...
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bada rabarin cewa idan mutum ya ciyar da iyalinsa waɗanda ciyarwarsu ta wajaba a kansa, kamar...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan mutum ya rasu akin s...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa baya...
Daga Malik ɗan Aus ɗan Hadasan cewa shi ya ce: Na taho ina cewa waye zai canji dirhamomi? sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi alhali shi yana wurin Umar ɗan Kha...
Tabi'i Malik ɗan Aus yana bada labari cewa shi ya kasance a wurinsa akwai zinarai, kuma yana son ya canja su da azirfofi, sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi -...
Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai bayan (azimin) Ramadan, ita gwargwadan Sa'i ne (wanda) awonsa yakai...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Allah Ya ce: Ya kai Ɗan Adam, ka ciyar zan ciyar da kai.
Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan mutum ya rasu akin sa ya yanke sai dai daga abu uku: Sadaka mai gudana, ko wani ilimin da ake anfanuwa da shi, ko ɗa na gari da ya ke masa addu'a".
Daga Malik ɗan Aus ɗan Hadasan cewa shi ya ce: Na taho ina cewa waye zai canji dirhamomi? sai Ɗalha ɗan Ubaidullahi alhali shi yana wurin Umar ɗan Khaɗɗab - Allah ya yarda da su - ya ce: Ka nuna mana zinarenka, sannan kazo mana, idan ɗan aikinmu ya zo, zamu baka azirfarka, sai Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: A'a, wallahi kodai ka ba shi azirfarsa, ko ka dawo masa da zinarensa, domin cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu".
Daga Ɗan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah.
Daga Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya ce; Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso Madina sai mutane suka fuskanto gare shi, aka ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya iso, sau uku. Sai na zo a cikin mutane dan inyi kallo, lokacin da na gane fuskarsa, sai nasan cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci bace, farkon abinda na fara jinsa ya yi magana da shi cewa ya ce: "Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Yaku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce: {Yaku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
[al-Mu'uminun: 51] .
Kuma Ya ce: {Yaku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku} [al:Baƙara: 172] sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya saurarawa wanda yake cikin mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (da bashinsa), Allah Zai inuwantar da shi a ranar Alƙiyama ƙarƙashin inuwarssa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa".
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah Ya yi wa mutum rahama mai saukakawa idan zai siyar, kuma idan zai siya, kuma idan zai nemi biyan bashi".
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu), sai ya gamu da Allah sai Ya yafe masa".
Daga Khaulat Al-Ansariyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai wasu mutane suna kutsawa a dukiyar Allah ba tare da wani haƙƙi ba, to, wuta ta tabbata a garesu ranar al-ƙiyama".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi, azimi garkuwa ne, idan yinin azimin ɗayanku ya kasance to kada ya yi kwarkwasa kada ya yi zancen banza, idan wani ya zage shi ko ya yi faɗa da shi, to ya ce lallai ni mai azimi ne, na rantse da wanda ran (Annabi) Muhammad yake a hannunSa, bashin bakin mai azimi shi ne mafi ɗaɗi a wurin Allah daga ƙanshin almiski, mai azimi yana da farin ciki biyu da zai yi farin ciki da su: Idan zai yi buɗa baki zai yi farin ciki, kuma idan ya gamu da Ubangijinsa zai yi farin ciki da aziminsa".