/ Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi

Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi

Daga Abu Mas’ud Allah Ya yarda da shi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Idan mutum ya ciyar da iyalinsa yana mai nemi ladan hakan, to, [za ta kasance] sadaka ce a ga reshi
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bada rabarin cewa idan mutum ya ciyar da iyalinsa waɗanda ciyarwarsu ta wajaba a kansa, kamar matarsa da iyayensa da ‘ya’yansa da sauransu, yana mai neman kusanci zuwaga Allah da hakan, yana neman ladan ciyarwar a wurin Allah, to, Allah zai ba shi ladan sadakarsa.

Hadeeth benefits

  1. Samun lada idan aka ciyar da iyali.
  2. Mumini [na gaskiya] yana neman yardar Allah a aikinsa da kuma lada da sakamakon da yake wurin Allah.
  3. Ya kamata a halarto da niyya mai kyau a kowanne aiki, daga cikin hakan akwai lokacin ciyar da iyali.