- Dukiyoyin da ke hannun mutane su ne dukiyar Allah, Ya sanyasu mamaya a kansu don su ciyar da su ta hanyar da aka shara'anta, kuma su nisanci tasarrufi a cikinsu da ɓarna, wannan ya game shugabanni da wasunsu cikin ragowar mutane.
- Tsanantawar shari'a a dukiyar al'umma, kuma cewa wanda ya jiɓinci wani abu daga cikinta, to, za a yi masa hisabi a ranar al-ƙiyama a kan samota da kuma ciyar da ita.
- Wanda yake tasarrufi tasarrufin da ba na shari'a ba a cikin dukiya ya shiga cikin wannan narkon, duka ɗaya ne dukiyar ta kasance tasa ce ko ta waninsa ce.