- Cikar Allah - Mai girma da ɗaukaka - a cikin zatinSa, da siffofinSa, da ayyukanSa, da hukunce-hukuncenSa.
- Umarni da tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da bin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Anfani da abinda yake ƙarfafa gwiwa akan aiki, inda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi", idan mumini ya san cewa wannan yana daga abubuwan da aka umarci Manzanni to cewa shi zai ƙarfafu zai ji ƙwarin gwiwa akan riko da shi.
- Daga abubuwan da suke hana amsa addu'a (akwai) cin haram.
- Daga sabubban amsa addu'a (akwai) abubuwa biyar:
- Na farkonsu: Tsawaita tafiya dan abinda ke cikinta na karyewar zuciya wanda shi yana daga mafi girman sabubban amsa addu'a.
- Na biyu: Halin buƙatuwa.
- Na uku: Ɗaga hannaye zuwa sama. Na huɗu: Nacewa Allah da maimaita ambatan RububiyyarSa, kuma shi yana daga mafi girman abinda ake neman amsa addu'a da shi. Na biyar: Daddadan abin ci da abin sha.
- Cin halal mai tsarki yana daga sabubba masu taimakawa ga aiki na gari.
- AlƘali ya ce: Mai tsarki kishiyar mummuna ne, idan Allah Maɗaukakin sarki ya siffanta shi da shi ana nufi da shi cewa shi abin tsarkakewa ne daga dukkanin tawaya abin tsarkakewa daga aibuka, idan aka siffanta bawa da shi kai tsaye ana nufi da shi cewa shi mai tsiraita ne daga munanan ɗabi'u kuma mai siffantuwa da kishiyoyin hakan, idan aka siffanta dukiyoyi da shi ana nufin kasancewarta halal ce kuma tana daga zaɓaɓɓun dukiyoyi.