Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji ba...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda ya ziyarci Dakin Allah - Madaukakin sarki - da Hajji kuma bai yi kwark...
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, am...
Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance idan ya yi nufin shiga aikin Hajji ko Umarah ita ce ya ce: (AmsawarKa ya...
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwar...
Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi, yana bayyana ayyuka na ƙwarai a goman farko na watan and Zul Hijja (Watan babbar Sallah) ya fi a ka...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da yaƙar kafirai, da yin ƙoƙari a fuskantarsu ta kowace hanya gwargwadan iko dan k...
Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da barin abinda kake kowanto a cikinsa na maganganu da ayyuka cewa shi an hana ne...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya yi Hajji bai yi kwarkwasaba, kuma bai yi fasikanciba zai dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi".

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai cewa godiya da ni'ima na Ka ne kuma mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya" Ya ce: Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: AmsawarKa amsawarKa, da taimakonKa (akan aiki), alheri yana hannayenKa, amsawarKa fata yana gareKa da kuma aiki.

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan kwanakin". Wato kwanaki goman, (Zul Hijja) Suka ce: Ya Ma’aikin Allah, Har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah ? Ya ce: Har Jihadi domin ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da komai ba.

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".

Daga Abul Haura'u al-Sa'adi ya ce: Na cewa Hassan ɗan Ali - Allah Ya yarda da su -: Me ka haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -? ya ce: Na haddace daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".

Daga Abu bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.

Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Farkon abinda za’a yi huknci a tsakanin mutane a ranar Alkiyama akan jini ne".