Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".
Bukhari da Muslim suka Rawaito shi
Bayani
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Yana kishi kuma Yana ki, kamar yadda cewa mumini yana kishi yana kuma ki, kuma cewa sababin kishin Allah shi ne mumini ya zo wa abinda Allah Ya haramta akansa na alfasha kamar ; zina da liwadi da sata da shan giya da wasunsu na alfasha.
Hadeeth benefits
Gargadarwa daga fushin Allah da kuma ukubarSa idan an keta alfarmarSa.
Share
Use the QR code to easily share the message of Islam with others