- Mafi girman zunubai shi ne yi wa Allah shirka; domin haka ya sanya shi farkon zunubai, kuma mafi girmansu, faɗinSa - maɗaukakin sarki yana ƙarfafa wannan: {Lallai Allah ba Ya gafartawa a yi shirka da shi, Yana gafarta koma bayan hakan ga wanda Ya so}.
- Girman haƙƙoƙin mahaifa, don Ya gwama haƙƙinsu da haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki -.
- Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin laifin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddodi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narkon shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasunsu sun fi wasu muni a haramci, ƙananan zunubai kuma su ne waɗanda ba wadannan ba.