- Kwaɗaitarwa akan yaƙar mushrikai da rai da dukiya da kuma harshe; kowa gwargwadan ikonsa, kuma yaƙi ba ya taƙaituwa akan yaki da rai kadai.
- Umarni da yaƙi na wajabci ne, zai iya zama wajibi aini (akan kowa da kowa), kuma zai iya zama wajibi kifa'i (wasu sun ɗaukewa wasu).
- Allah Ya shar’anta jihadi saboda wasu al'amura daga cikinsu: Na farko: Faɗa da shirka da mushrikai; domin cewa Allah ba Ya karɓar shirka har abada.
- Na biyu: Kawar da wahalhalun da suke bijirowa hanyar kira zuwa ga Allah.
- Na uku: Kiyaye aƙida daga dukkan abinda yake kishiyantarta.
- Na huɗu: Kariya ga musulmai da ƙasashensu da mutuncinsu da kuma dukiyoyinsu.