- Rantsuwa mai dulmiyarwa ba ta da kaffara; don tsananin haɗarinta da girmanta, kawai dai akwai [damar] tuba a cikinta.
- Taƙaituwa a kan ambaton waɗannan manyan laifukan guda huɗu a hadisin [ya kasance] don girman laifinsu ne, ba don su ne kadai ba.
- Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin zunubin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narko da shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasu sun fi wasu muni a haramci.
- Kananan zunubai su ne waɗanda ba waɗannan ba.