- Allah - AlherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ƙetare kuma Ya yi afuwa daga tunani da zantukan zuci waɗanda suke ɗarsuwa a zuciya, sai mutum ya zantar da ransa da su, kuma su wuce haka akan tunani.
- Saki idam mutum ya yi tinaninsa, ya bijiro a cikin tinaninsa, sai dai bai fadama kowa ba kuma bai rubuta shi ba, to ba'a ɗaukarsa a matsayin saki.
- Zancen zuci ba'a kama mutum da shi duk girman da ya yi muddin dai bai tabbata a cikin ransa ba, ya yi aiki da shi ko ya zantar da shi.
- Girman darajar al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da keɓantarta da rashin kamawa da zancen zuci saɓanin al'ummun da suka gabata.