Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita a ranar idi zuwa wurin sallah, ya kasance haƙiƙa ya yi wa mata alƙawarin cewa zai wares...
Daga Uƙubah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da shiga wurin...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga cakuɗuwa da mata ajanibai (waɗanda ba muharramai ba), ya ce: Ku kiyaye kawunan...
Daga Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Babu aure sai da waliyyi".
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa mace auranta ba ya inganta sai da waliyyin da zai tsaya a ɗaurin auren.
Daga Nana Aisha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: “Duk macen da ta yi...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar da mace ta aurar da kanta ba tare da izinin waliyyanta ba, kuma cewa auranta ɓatacc...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya zo wa matarsa ta dubu...
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar daga miji ya zo wa matarsa ta duburarta; cewa shi tsinanne ne abin korewa daga rah...
Daga Abu Sa'ida Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita zuwa wurin da ake sallah, a babbar sallah ko a ƙarama, sai ya wuce inda mata suke, sai ya ce: "Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba", suka ce: To menene tawayar Addininmu da hankalinmu ya Manzon Allah? ya ce: "Shin yanzu bai zama cewa shaidar mace kwatankwacin rabin shaidar namiji ba ce" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar hankalinta, shin yanzu idan ta yi al’ada ba ta sallah ba ta azimi" suka ce: Eh, ya ce: "To wannan yana daga tawayar Addininta".
Daga Uƙubah ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haneku da shiga wurin mata" sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin ƙanin miji fa? ya ce: "Ƙanin miji (shi ne) mutuwa".
Daga Nana Aisha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: “Duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyinta ba, to aurenta ɓatacce ne - sau uku - idan ya tare da ita, to sadakin ya kasance nata ne saboda abinda ya samu na (jima'i) daga gareta, idan suka yi jayayya to sarki (shi ne) waliyyin wanda ba shi da waliyyi".
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne".
Daga Uƙubah Ibnu Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Mafi cancantar sharuɗɗa da za ku cika; su ne wadanda aka halatta muku mata da su.
Daga Abdullahi Ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Duniya jin daɗi ce, fiyayyen jin daɗin duniya shi ne mace ta gari.
Daga Jariri ɗan Abadullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da gani na fuj'a sai ya umarceni in juyar da ido na.
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi layya da raguna biyu masu farar fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da hannunsa, kuma ya ambaci Allah ya yi kabbara, ya ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu.
Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".
Daga AbdurRahman Dan Abu Laila cewa sun kasance a wajen Huzaifa, sai ya nemi a shayar, sai wani Bamajushe ya shayar da shi, lokacin da ya ajiye ƙwaryar a hannunsa sai ya jefe shi da ita, kuma ya ce: Da badan ni na hana shi ba, ba sau ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba - kamar cewa shi ya ce: Ban aikata wannan ba -, sai dai cewa ni na ji annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira".
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".