- Haramcin zakkewa mata ta duburarsu.
- Jin daɗi daga mata a koma bayan duburarta na jikinta ya halatta.
- Musulmi yana zakkewa mace ne ta farjinta kamar yadda Allah Ya umarce shi; amma ta dubura to a cikin hakan akwai ɓata ɗabi'a, da tozarta zuriya, da saɓawa abinda nagartattun ɗabi'u suke a kansa, da kuma cutuka masu kaiwa ga ma'auratan.